Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Nijar Ta Rufe Dakunan Kwanan Daliban Jami'ar Yamai


Daliban Jami'ar Yamai da ke ficewa daga dakunan kwanansu da aka rufe

Shekara daya bayan da daliban Jami'ar Yamai suka yi zanga-zangar da ta yi sanadiyar mutuwar dalibi daya, jiya Laraba daliban sun sake yin wata zanga-zangar inda suka yi fito-na-fito da 'yan sanda da fashe-fashen wasu motoci yayin da wasusun suka jikata har gwamnatin kasar ta yanke shawarar rufe dakunan kwanansu.

Bayan wani mummunan bata kashi da ya auku tsakanin daliban Jami'ar Yamai da 'yan sanda, ministan ilimi mai zurfi ya bayyana cewa gwamnatin Nijar ta yanke shawarar rufe wurin kwanan daliban har zuwa lokacin da aka tabbatar kura ta lafa.

A cewar ministan lokacin zanga zangar daliban sun yi fashe fashen motoci har da wata ma'aikata saboda haka gwamnati ta ga ya wajaba a rufe dakunan kwanan na dalibai har sai abun da hali ya yi.

Sai dai hankalin daliban da suka fito daga yankin karkara ya tashi saboda wai basu da kowa a Yamai.

Dalili ke nan da wani dalibi Abdu Musa Shehu ya kira gwamnati da ta canza tunaninta.

Ya ce shi kansa daga Tahoua ya fito bashi da inda zai samu ya fake.

Sai dai ministan ilimin ya ce za'a ci gaba da ba da karatu a Jami'ar. Haka ma ba'a rufe dakin cin abinci ba, kazalika ma babu wani aikin Jami'ar da aka dakatar ba ya ga rufe dakunan kwanan daliban.

Kungiyar dalibai ta sanar cewa dimbin dalibanta ne suka ji rauni sakamakon arangamar da suka yi da 'yan sanda. Akwai wasu da dama kuma da suke tsare a wurin 'yan sanda.

Ko da yake ba'a ba da alkaluman wadanda suka jikkata ba, ministan ilimi mai zurfi ya ce za'a gudanar da bincike akan lamarin da ya faru a jiya Laraba.

Duk wanda aka samu da laifi za a gurfana gaban shari'a, a cewar shi.

Zanga zangar ta jiya ta zo ne a daidai lokacin da daliban ke matsawa gwamnati ta hukumta wadanda suke da hannu a mutuwar wani dalibi a yayin zanga zangarsu ta watan Afirilun shekarar 2017.

Bugu da kari, daliban na kukan rashin biyansu alawus dinsu tare da karancin motocin jigila da wasu kayan aiki.

Ga rahoton Souley Barma da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:50 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG