Accessibility links

Gwamnatin Nijer Ta Bayyana Shirin Kafa Sababbin Kotuna A Kauyuka


Hukumomi a jamhuriyar Nijer, sun bayyana shirin kafa wasu sabbin kotuna a garuruwa da dama da nufin kara kusantar da jama’a ga mashara’anta ta yadda za a kawo karshen tsaikon da sha’anin shara’a ke fuskanta wajan matsalar yawan jeka ka dawo dake haddasawa mazaunan karkara cikas.

Samar da kotunan daukaka kara a cikin manyan biranen jihohi Takwas tare da soke zaman shekar- shekara a jamhuriyar Nijer, na daga cikin irin matakan da gwamnatin kasar ta bayyana shirin dauka domin magance matsalolin shari’a.

Malam Nasiru Saidu, ya bayyana cewa talakawa na yawan koke koke akan yadda sai mutuum ya yi tafiya mai nisa kafin ya sami biyan bukata a bangaren shari’a, dan haka idan gwamnati ta kudiri aniyar kafa kotuna a wadannan jihohi, abu ne da talakawa zasu kara da hannu biyu.

Domin kusantar da kotunanj shari’a kusa da jama’ar karkara, gwamnati ta kudiri aniyar bude kotunan a yankunan karkara.

Dan majalisar dokokin kasa Malam Shitu Mammam, ya bayyana gamsuwa da matakin tare da shawartar hukumomi su dauki matakan amfani da na’urorin zamani wajan ayyukan bada takardu irin su takardun haihuwa a daukacin kotunan kasar ta Nijer.

Wakilin muryar Amurka a yamai Sule Mumuni Barma ya aiko mana Karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:38 0:00

Facebook Forum

An Yi Jana’izar Idriss Deby Yayin Da Makomar Chadi Ke Cike Da Rashin Tabbas
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:38 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
Yadda Aka Kashe Sojojin Najeriya 11 A Jihar Benue Da Ke Arewacin Kasar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
Wani Sirri Da Tsohon Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou Ya Fadawa ‘Sarki Sanusi II’
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:23 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG