Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Nijer Ta Kaddamar Da Shirin Gina Gidaje 2,500 Domin Masu Karamin Karfi


Gwamnatin jamhuriyar nijer ta bayyana shirin gina gidaje 2,5000 a tsawon shekaru biyar masu zuwa a wani yunkurin takaita wahalhalun ‘yan kasar a game da matsalar hayar da ake fama da ita

Matsalar ta mamaye manyan birane inda samin gidan haya ke kokarin fin karfin talakka har ma da kananan ma’aikata sai dai ‘yan adawa sun bayyana shirin gwamnatin a matsayin yaudarar siyasa.

Aikin gine ginen wanda gwamnatin ta kaddamar a lokacin wani taro da firayin ministan kasar Brigi Rafini ya jagoranta, wanda kuma aka bayyana a matsayin alkawarin da shugaban kasar Mahamadou Issoufou ya dauka a lokacin yakin neman zabe, zai bayar da damar gina gidaje a kowace shekara har na tsawon shekaru biyar a fadin kasar a matsayin ba masu karamin karfi damar mallakar gidajen kansu a lokacin da matsalar hayar ke cigaba da tsananta.

Ministan raya biranen kasar Kasim Muktar, yace mallakar gida ta zama babbar matsala, shiyasa suka kaddamar da wannan tsari na saukakawa jama’a domin su mallaki gidajen kansu, kuma za’a samarwa da mutane dubu 2,5000 gidaje a cikin shekaru biyar.

Kungiyoyin kwadagon kasar sun iy na’am da wannan shiri mai muhimmanci sai dai da alamun shakka a tare da su dangane da cikar wannan buri kamar yadda sakataren hadaddiyar kungiyar kwadagon kasar ya bayyana cewa suna matukar alfahari da ganin gwamnati ta cika wannan alkawari.

Kodashike yak ara da cewa, kwanakin baya gwamanatin ta ce zata gina gidaje dubu a kowace shekara, sai gashi daga karshe guda dari hudu kacal aka gina suma na sojoji ne.

Gwamnatin ta tabbatar da cewa ta dauki kwararan matakan kaucema duk wata matsala, koda shike Alhaji Rabilu Kane na Jam'iyya mai adawa ya ce wanda yayi alkawari gina gidaje dubu cikin shekaru biyar kuma ya gaza, babu yadda za'a yi ya gina gidaje dubu ashirin da biyar cikin shekaru biyar, wannan siyasa ce tare da yaudara.

Gwamnati ta bukaci mabukata a duk inda suke su yi rajista ko a yankunan da suke kokuma a ofisoshin jakadancin kasar dake wasu kasashe.

Ga rahoton Sule Mumini Barma daga Jamhuriyar Nijer.

XS
SM
MD
LG