Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Oyo Tayi Barazanar Kwace gonakin da ba a nomawa


Wani yana tsaye kusa da wani fili a Najeriya
Wani yana tsaye kusa da wani fili a Najeriya

Gwamnatin jihar Oyo tace zata kwace duk gonaki ko gandun dajin da ba a noma ba, kuma ba a yi wani amfani da shi ba a jihar Oyo

Gwamnan jihar Abiyola Ajimobi ne ya bayyana haka a wani jawabi da yayi wa manoma.

Gwamna Ajimobi yace “muna gabatar maku da zabi a matsayinsu na wadanda suka mallaki kasa, ko dai ku hada guiwa da gwamnati, ko ku hada kai da masu zuba jari, ko ku bada filayenku haya, ko ku noma gonakinku”

Gwamnan yace gwamnti zata kwace gonakinsu idan suka barsu suka zama gandun daji kawai ba tare da kulawa ko amfani dasu ba. Bisa ga cewarshi, gwamnati zata yi amfani da irin wadannan gonakin idan ta karba wajen noma abinci da zai amfani jama’a.

Da suke maida martani, wadansu manoma da Sashen Hausa ya yi hira dasu sun bayyana gamsuwa da matakin da gwamnatin ta bayyana shirin dauka, domin bisa ga cewarsu, sau da dama mutane sukan sayi filaye basu da wani shiri ko bukatar amfani dasu sai su kyalesu su zama da hadari ga al’umma.

Sai dai wadansu suna gani wannan umarni zai tauyewa talakawa ‘yancin mallakar filaye kasancewa basu da karfin sayen fili da tada gini nan take. Suka kuma shawarci gwamnati ta samar da hanyar taimakawa masu karamin karfi domin su iya kula da filayen da suka mallaka.

Ga cikkaken rahoton da wakilinmu Hassan Umaru Tambuwal ya aiko daga Ibadan, Jihar Oyo,

Gonatki a jihar Oyo-2;27"
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG