Accessibility links

Gwamnatin Taraba ta Sassauta Dokar Hana Fita a Wukari


Mukaddashin gwamnan Taraba Alhaji Garba Umaru.

Biyo bayan koke-koke da al'ummar Wukari suka dinga yi domin dokar hana fita ba dare ba rana da gwamnatin jihar ta saka masu, yanzu sun samu dan sassauci kafin a ga abun da ka iya faruwa nan gaba,

A sanarwar da gwamnatin Taraba ta fitar tace ta dauki matakin sassauta dokar hana fita din ne ganin irin halin da jama'ar yankin suke ciki.

Dokar hana fita ba dare ba rana ta haddasa rashin abinci da rashin ruwan sha da kuma bullar cututtuka. Mr Kefas Sule sakataren yada labarai na mukaddashin gwamnan jihar Alhaji Garba Umaru yace yayi zama da sarakunan yankin Wukari. Bayan zamansu mukaddashin gwamnan ya bukaci su bashi shawara akan maganar sassauta dokar. Yanzu mutane na iya walwala daga karfe shida na safe zuwa karfe goma sha biyu na rana.

Gwamnati ta shaidawa mutanen Wukari cewa ba sonta ba ne ta saka masu dokar amma ya zama dole a yi hakan domin a samu zaman lafiya. Bayan kwana uku idan babu wata ta'asa da ta sake kunno kai gwamnati na iya kara sassaucin.

Shugabannin yankin suna kira a hau teburin sulhu domin kawo karshen kashe-kashen da ake yi. Daniel Ishaya Gani wani dan majalisar jihar dake wakiltar yankin na Wukari yace a nemi shugabannin Miyatti Allah idan Fulani ne ke haddasa kashe-kashe da shugabannin addini a zauna dasu a warware matsalar. Idan kuma ba 'yan Najeriya ba ne sojoji su san yadda zasu fitarda su daga kasar. Duk wadanda aka yiwa barna a biyasu. Yakamata a nemi zaman lafiya domin mutane basa iya noma haka ma cikin garin babu lafiya. A zauna a ba juna hakuri.

Ita ma kungiyar Miyatti Allah tace a shirye take a zauna a tattauna domin a samu zaman lafiya. Kungiyar ta musanta zargin cewa ta yiwo hayar mayaka daga waje. Alhaji Mafindi Umaru Danburam shugaban Miyatti Allah a jihar Taraba yace suna son zaman lafiya idan za'a daina kai masu harin sari ka noke ana karkashesu da dabbobinsu.

An kara tura 'yan sandan kwantarda tarzoma a yankin da kuma karin sojoji dake yin sintiri akan hanyoyi.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.
XS
SM
MD
LG