WASHINGTON, D. C. - Ministan Lafiya da Walwalar Jama'a, Ali Pate, ne ya bayyana hakan sa'ilin da yake jaddada aniyar gwamnatin Shugaba Tinubu ta yiwa harkar kiwon lafiyar 'yan Najeriya garanbawul ta yadda zai dace dana sauran duniya.
A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun kakakin ma'aikatar, Deworitshe Patricia, ta fitar a jiya Lahadi a Abuja, Ministan yace, ba za'a iya samun nasarar yiwa harkar kiwon lafiya garanbawul da sabunta shi harma da samar da karin damammaki ba har sai an samu amincewar tsarin nan na hanu da yawa a bangaren lafiya (SWAP) da kuma tsarin sabunta zuba jari a bangaren lafiya (NHSRIP).
A cewar Ministan Lafiyar, a zantawarsa game da cigaban da aka samu a fannin kiwon lafiya a matakin farko a Najeriya a bisa tsarin swap, na hannu da yawa, nazarin da aka gudanar ya bayyana bukatar yin kwaskwarima ga tsarin gudanar da asusun kula da kiwon lafiya a matakin farko (BHCPF) da tsare-tsare da ayyukansa da tsarin bin diddigin yadda ake kashe kudade da kimarsa a idanun jama'a, inda yace dukkanin jihohin Najeriya da Abuja sun dukufa wajen kawo gyara, tare da shan alwashin inganta kiwon lafiyar 'yan najeriya.
Pate ya kara da cewar, za'a sake nazartar dokokin su kunshi tsarin kiwon lafiyar da ake baiwa al'ummar Najeriya a yayin da ake kokarin rage mace-macen mata yayin haihuwa da daukar nauyin kudin jinya daga aljihu tare da daidaita ingancin kiwon lafiya a kananan asibitoci.
Dandalin Mu Tattauna