Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Tarayya Ta Gaza Inji Dattawan Arewa Maso Gabas


Taron dattawan arewa maso gabas da jama'arsu a Abuja
A daidai lokacin da kungiyar kare hakin bil adama ta Amnesty International ta fito da rahoton dake cewa an aikata laifin yaki a arewa maso gabashin Najeriya sai gashi dattawan jihohin Borno da Yobe da Adamawa dake zaune a Abuja sun yi korafin cewa gwamnatin tarayya ta gaza wurin dakatarda kashe-kashen dake faruwa a yankinsu.

A cikin kasidar da ya gabatar Dattijo Al-amin Dagash tsohon hafsan hafsoshin sojojin mayakan sama ya bayyana alhininsa a fili tare da dasa ayar tambaya gameda yadda ake janye jami'an tsaro sa'o'i kadan kafin 'yan ta'ada su kai hari kamar yadda aka yi har aka kashe 'yan makaranta hamsin da tara a Buni Yadi cikin jihar Yobe. Haka ma ake anfani da jirage masu saukar angulu wajen kaiwa 'yan ta'ada makamai ba tare da jami'an tsaro sun daga ko yatsa ba, abun da dattawan suka ce alama ce ta sakacin mahukuntan kasar.

Alhaji Adamu Ciroma tsohon ministan kudi na gwamnatin tarayya yana daya daga cikin dattawan da aka yi taron da shi. Ya kira jami'an tsaro da su sabunta salo wajen kokarin shawo kan kalubalen tsaro.Yace a sake dubawa a ga menene yakamata a yi domin a shawo kan lamarin. Dangane da dokar ta baci yace an yi sau daya an yi sau biyu babu abun da ta tanada domin haka babu anfanin a cigaba da ita. Idan gwamnati bata yi sabon tunane ba to ko ba zata shawo kan lamarin ba.

Wannnan shi ne karo na farko da dattawan suka fito suka yi magana da kakkausan lafazi kan rikicin da ya dabaibaye yankinsu. Dr Shettima Mustapha yace duk abun da mutum ya sha yi bai samu nasara ba me yasa zai cigaba da yin sa. Yace a akasarin gaskiiya ma kashe-kashen da ake yi yanzu ya fi na lokacin da babu dokar ta baci.Saboda haka babu wani dalilin cigaba da dokar ta baci a yankin.

Masu ruwa da tsakin dai sun yi karin bayyani. Sun ce tun daga shekarar 2009 kawo yanzu an raba mutane fiye da miliyan uku da muhallansu yayin da kuma aka kashe rayuka sama da dubu goma sha biyar yawancinsu farar hula abun da yasa sakataren gwamnatin jihar Borno yace gwamnatin tarayya ta fi ta jihohi laifi domin ita ce ke da madafin iko. Yace duk jami'an tsaro da hukumomin kwastan da na shige da fici duk suna hannun shugaban kasa ne ba hannun gwamnan jiha ba. Domin haka idan kowane cikin wadannan basu yi aikinsu ba laifin gwamnatin tarayya ne. Yace masu ba shugaban kasa shawara yakamata su duba kundun tsarin milkin kasar su sanarda shi ikon da yake da shi.

Dattawan sun ce zasu cigaba da takarawa wajen taimakawa al'ummar yankinsu da yanzu ke fuskantar barazanar yunwa da rashin abinci.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:19 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG