Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Tarayya Ta Shirya Ba Kananan 'Yan Kasuwa Lamunin Naira 150bn


Gwamnan Bauchi M.A. Abubakar wanda ya kaddamar da shirin gwamnatin tarayya na baiwa kananan 'yan kasuwa tallafi da lamunin kudi

Gwamnan Bauchi Barrister Muhammad Abdullahi Abubakar yayinda yake kaddammar da shirin na yankin Bauchi yace gwamnatin tarayya ta fito da shirin ne da zummar taimakwa kananan 'yan kasuwa da jarinsu bai kai ba ko kuma dama can basu da jarin na cigaba da kasuwanci.

Inji gwamnan rancen za'a baiwa 'yan kasuwan da ada can suna cikin kasuwanci amma saboda canje canjen yanayi watakila jarinsu ya fara komawa baya.

Irin mutanen ne za'a tallafawa domin su bunkasa jarinsu samu su fadada kasuwanci.

A jihar Bauchi mutane dubu arba'in ne zasu anfana daga lamunin. A bankin masana'antu na kasa nan ne gwamnatin tarayya ta ajiye kudaden Naira biliyan dari da hamsin saboda a rabawa 'yan Najeriya.

Lamunin dai bashi da ruwa. Abun da aka ba mutum shi ne zai mayar cikin watanni shida. Gwamnan yace dole a yi hattara domin ba bashin da mutum zai dauka ba ne ya je yana kara mata.

Alhaji Mansur Manusoro mai tallafawa gwamnan jihar Bauchi akan kungiyoyi da masana'antu yayi bayani akan matsayin gwamnatin jihar dangane da shirin samar da lamunin.

Inji Alhaji Mansur suna aiki da bankin masana'antu da kuma hukumar da aka dorawa alhakin tantance masu sana'a kafin a basu kudi. Rance mafi kankanci shi ne Naira dubu goma mafi yawa kuma dubu dari ne.

Duk wanda ya kasa biyan bashin shugabannin kungiyarsa za'a kama su biya.

Wasu da suka anfana da lamunin sun tofa albarkacin bakinsu. Wata da take sana'ar sayar da ruwa da yin zoborodo ta samu dubu hamsin tace kudin zai taimaka mata bunkasa sana'ar. Sun kuma amince da tsarin biyan bashin.

Ga rahoton Abdulwahab Muhammad da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:20 0:00

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG