Accessibility links

Gwamnatin Tarraya Ta Damu Saboda Barkewar Cutar Kwalera


Mace dauke da danta mai fama da cutar kwalara

Gwamnatin tarayya ta baiyyana damuwar ta bisa ga karuwar yawan mutuwa daga barkewar cutar kwalera a kauyen Namu cikin karamar hukumar Qua’pan a jihar Plato.

Gwamnatin tarayya ta baiyyana damuwar ta bisa ga karuwar yawan mutuwa daga barkewar cutar kwalera a kauyen Namu cikin karamar hukumar Qua’pan a jihar Plato. Mataimakin Directa na kauda cututtuka, ma’aikatar lafiya ta kasa, Dr Moses Anefiong, ya bayyana damuwar a lokacin zagayar sassan da suka kamu da cutar.

Dr. Moses yace, Ma’aikatar lafiya ta damu yadda har yanzu duk da ci gaban da aka samu a fannin ayyukan jinya mutane ke ci gaba da mutuwa ta wajen cutar kwalera. Yayi gargadi da cewa, yayinda gwamnati take yin kokarin tanada ruwan sha mai kyau bai kamata mutane suyi watsi da kula da lafiyarsu ba. Yace abu mafi sauki da ya kamata su rika yi shine wankin hannu kamin cin abinci, bayan zuwa bayan gida, kuma su rufe abincinsu daga kudaje. Bayan wannan duka, mutane dole su dauki tsabta da mahimmanci. Wadannan abubuwa masu sauki ne, amma da mahimmanci kwarai.

A wani gefe kuma Kwamishinan yada labarai na jihar Legas, Mr Lateef Ibirogba, yace gwamnatin jihar ta shiga yaki sosai da cutar kwalara kuma tana hada hannu da ma’aikatun lafiya, da kuma ma’aikatar kuka da tsabtace muhalli na jihar domin shawo kan matsalar.

Yayinda yake magana kan ci gaba da duba kauyuka da suke fama da cutar, Mr Ibirogba yace gwamnatin jihar ta sayo magunguna, ta kuma rarraba su ga asibitoci dake kananan hukumomin jihar, domin kauda cutar.

Wani mataki kuma da gwamnatin jihar Lagos ta dauka na shawo kan matsalar yaduwar cutar kwalar a jihar ita ce yin kokarin koyawa mazauna yankunan karkara akan kare barkewar cutar.
XS
SM
MD
LG