Accessibility links

Gwamnatin Tarayyar Najeriya Ta Kaiyyana Karuwar Ciwon Hanta


Wata mata mai fama da cutar hanta

Gwamnatin tarayya ta baiyyana karuwar kwayar cutar hepatitis a kasar Najeriya

Gwamnatin tarayya ta baiyyana karuwar kwayar cutar hepatitis a kasar Najeriya.

Wannan ya biyo wani bincike da mai’aikatar yaki da cututtuka wadda ta sami goyon bayan kunigyar hada magunguna ta Roche ta gudanas kwanan nan a Nijeriya. Binciken ya nuna cewa Hepatitis B na da 11 daga cikin 100 kana kuma Hepatitis C na da Kashi 2.2 a cikin 100 a Nijeriya.

Ance cututtukan sunfi yawa a sashin kasashen Afrika kudu da sahara, inda yawan masu dauke da kwayoyin cututtukan ya kai kimanin kashi 10-20 daga cikin 100 na yawan jama’a.

Yayinda hepatitis B na da maganin rigaki, babu wani magani a yanzu da za’a iya yin amfani da shi a matsayin rigakafi na hepatitis C.

Sai dai kuma a wani dandali na tattaunawa da jan jaridu da kuma kaddamar da kungiyar yaki da Hepatitis a Nijeriya mai taken “Yaki da karuwar Hepatitis a Nijeriya”, ministan lafiya, Farfesa Onyebuchi Chukwu yace, “Mataki kan karuwar kwayar cutar hepatitis a Nigeriya,” yace gwamnatin tarayya na shirye ta bi diddigin wannan batun.

Ya koka ganin yadda a duniya baki daya ba’a maida hankali a kan hepatitis da nunin cewa hepatitis yafi HIV/Kanjamau hatsari.

Chukwu yace, “fiye da mutane biliyan biyu sun kamu da kwayar cutar hepatitis B a duniya baki daya, yayinda mutane miliyan 280 da kwayar cutar ta rigaya ta shiga hantar su. Mutane wajen miyan 2 da ke dauke da wannan kwayar cutar ne suke mutuwa a kowace shekara sakamakon ciwon hanta ko kuma kansar hanta wadda kwayar cutar ta haddasa.

“Abi takaicin shine, a duniya baki daya har ma da Nijeriya, ba’a damu da daukar matakai domin kawo karshen wanna cutar duk da ganin cewa hepatitis sai kara habaka yake yi da kuma ganin cewa za’a iya yi wa cutar rigakafi.”

Chukwu ya lura da cewa koda yake cutar kanjammau tana jan kudi kimanin dola 2,74 akan kowanne mutum mai rayuwa da kanjamau kowacce shekara, kimanin dola 20 ne kawai ake batarwa a kan masu cutar hepatitis.

Chukwu, wanda pamanent sakatare na maaikatar lafiya Ambasada Sani Bala ya wakilta, yace wannan kwamitin wani murtani ne da gwamnati ta bullo da shi domin yaki da wannan kwayar cutar.
XS
SM
MD
LG