Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Trump Ta Gargadi Haramtattun Bakin Haure Su Koma Gida Don Su Iya Dawowa Kasar Cikin Mutunci Nan Gaba.


Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump

Gwamnatin Trump ta fito da wata sabuwar manhaja da zata ba baki 'yan cirani dake zaune a Amurka ba bisa ka’ida ba damar maida kansu gida, maimaimakon fuskantar kamu da tsarewa, wani abu dake dorawa kan shirin shugaba Donald Trump na maida bakin haure kasashen su.

A ranar Litinin ne Gwamnatin Trump ta fito da wannana sabuwar manhaja wanda a fadin mahukunta zata ba mutanen dake zama Amurka ba bisa ka'ida ba damar kai kansu kasashen su.

Manhajar da jami’an kwastan da masu tsaron kan iyakoki ta Amurka da ake kira CBP Home, zata bada zabi ga duk wani wanda ke da niyyar brin kasar, in ji hukumar.

‘’Manhajar ta CBP Home zata ba bakin haure zabin fita daga kasar a yanzu bisa rajin kan su, yadda za su samu damar komowa nan gaba ta halattaciyar hanya su kuma nemi arzikin su a kasar ta Amurka, a cewar, sakatariyar ma’aikatar tsaron cikin gida Kristi Noem cikin wata sanarwa. Ta kara da cewa,’’ idan kuma suka ki, to za mu nemo su mu maida su kasashen su, kuma ba za su kara dawowa ba har abada.’’

Trump na jam’iyar Republican ya sha alwashin sai ya maida dimbin bakin haure dake zaune a Amurka ba bisa ka’ida ba zuwa kasashen su.

Haka zalika Gwamnatin ta Trump ta dauki wasu matakan da ka iya mastin lamba ga bakin hauren dake zaune a kasar ba bisa ka’ida ba na ficewa daga Amurka.

Wani tsarin daidaita lammurra na Gwamnatin Trump da ake sa ran zai fara aiki a ranar 11 ga watan Afrilu ya bukaci mutanen dake zaune ba bisa ka’ida ba a kasar su yi rajista da Gwamnatin Tarayya ko su fuskanci tara ko dauri.

Manhajar CBP Home ta maye gurbin wanda aka sani a baya da CBP wanda aka kaddamar a karkashin gwamnatin Biden. Manhajar ta zamanin Biden ta hada da wasu tsare tsare da suka bayar da dama ga wasu bakin haure milyan guda a Mexico damar samun damar neman shiga Amurka ta halattattun hanyoyin kan iyaka.

'Yan Republican sun caccaki shirin na Biden, cewa, hakan ya karfafa dandazon bakin haure shigowa cikin Amurka ba tare da yin wani wadataccen shiri ba domin hakan.

Shigar Trump ofis da sa’a guda ya yi fatali da CBP, lamarin da ya bar bakin hauren dake jiran a saurari uzurin su cikin rashin tabbas da rashin sanin inda za su dosa.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG