Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Turkiya Ta Sake Sallamar Ma'aikatanta Dubu Goma


Shugaban Kasar Turkiya Recep Tayyip Erdogan

Gwamnatin kasar Turkiyya ta sake sallamar kimanin ma’aikatan gwamnati da yawan su ya kai dubu goma, yayinda take ci gaba da gamawa da mutanen da take zargi da taka rawa a yunkurin juyin mulki da aka so yi a kasar cikin watan Yulin wannan shekara.

Labarin sallamar ma’aikatan da suka hada da manyan malaman makarantu da kanana,da jami’an kiwon lafiya, ya bayyana ne a jiya lahadi

Kafin zuwa yanzu, hukumomin na Turkiyya sun kori ma’aikata farin kaya da yawan su ya kai dubu 80, kana an tsare sama da dubu 30 wadanda ake gani suna da alaka da juyin mulkin.

Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya fada ya nanata cewa malamin nan dake zaune a nan Amurka Fetullah Gullen yana da hannu dumu-dumu cikin yunkurin juyin mulkin, wanda yayi dalilin murtuwar mutane a kalla 270.

Shi ko Gullen dattijo ne dan shekaru 75 da haihuwa ya jima yana zaman gudun hijira a nan Amurka tun a cikin shekarar 1999, kuma ya nisanta kansa da wannan zargin na juyin mulki, wanda kasar ta Turkiyya ke naman a tasa keyarsa zuwa gida.

Shugaba Obama dai ya shaidawa Erdogan a taron kasashen nan na G-20 a farkon wannan shekarar a nan Washington DC cewa Amurka a shiryetake ta marawa Turkiyya baya game da binciken wannan yunkurin juyin mulki amma fa batun tasa keyar wani zuwa gida Turkiyya, wajibi ne hakan ya cika sharudda umurnin kotunan Amurka.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG