Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Turkiyya Ta Yi Luguan Wuta a Syria


Wasu Dakarun Turkiyya a Zaune Cikin Shiri

Wasu masu fafutuka a kasar Syria sun ce dakarun Turkiyya sun yi lugudan wuta akan mayakan Kurdawa da ke arewaci na tsawon cikin kwanaki biyu a jere, bayan wani gargadi da suka yi na cewa za su dauki mataki idan har suka fuskancin wata barazana daga kan iyakar kasar.

Kungiyar nan mai sa ido a rikicin kasar mai suna Syrian Observatory for Human Rights, ta ce hare-haren sun fi maida hankali ne a yankin arewacin birnin Aleppo inda suka kashe mayaka biyu.

A jiya Asabar Firai ministan Turkey Ahmet Davutoglu ya ce mayakan Kurdawan, barazane ne ga garin Azaz da ke da ‘yar tazarar tafiyar kilomita daga kan iyakar kasar.

Dakarun Syria da ke samun goyon bayan Rasha na ci gaba da kutsa kai a yankin, a wani yunkuri na sake kwato garin Aleppo da kuma yankunan iyakar kasar.

Ita dai Turkiyya na yiwa jam’iyyar PYD da reshen mayakan ta na YPG kallon rassan jam’iyyar Kurdawa ta PKK da ta jima ta na kai hare-hare akan gwamnati.

XS
SM
MD
LG