Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnoni 3 Na PDP Na Kan Hanyar Komawa APC - Fani-Kayode


Femi Fani-Kayode ya koma APC.
Femi Fani-Kayode ya koma APC.

Tsohon ministan sufurin jiragen sama na Najeriya Femi Fani-Kayode ya ce akwai yiwuwar wasu gwamnoni 3 na PDP su sauya sheka zuwa jam’iyyar APC.

A yayin da ya ke amsa tambayoyin manema labarai jim kadan bayan ganawa da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, biyo bayan komawarsa jam’iyyar APC, Fani-Kayode ya ambaci gwamnonin jihohin Bauchi, Enugu da Oyo, da cewa za su iya bin sahunsa na sauya sheka zuwa jam’iyyar ta APC mai mulki.

“Idan ba za ku damu da ambaton sunaye ba, wasu kamar gwamnan jihar Enugu, da gwamnan jihar Oyo, da kuma babban aminina gwamnan jihar Bauchi, dukansu abokai na ne, kuma ina fatar za su biyo ta wannan tafarkin,” Fani-Kayode ya shaidawa manema labarai.

Sai dai ya kara da cewa ko sun sauya shekar ko basu sauya ba, za su ci gaba da yin aiki tare domin ci gaban Najeriya, da kuma ba da gudummuwa wajen yaki da ‘yan ta’addar da suka addabi ‘yan Najeriya.

Ya ce “wajibi ne mu kunyata bata-garin waje da suke son ganin muna fada da junan mu a kasar nan, suke kuma son maida kasar nan wani sansanin 'yan gudun hijira.”

Dangane da dalilinsa na komawa APC kuwa, Fani-Kayode ya bayyana cewa yana ganin wannan ne lokacin da ya fi dacewa da hakan, da kuma nuna yabawa da goyon baya akan wadanda suke ta kokari da fadi-tashin ganin Najeriya ta ci gaba, musamman ta fannin tsaro da yaki da ta’addanci.

“Babban muhimmin abu shi ne, dole ne mu kasance tsintsiya madaurinki daya, mu yi aiki tare domin mu kare kasarmu,” in ji Kayode.

Tsohon Ministan wanda a can baya yana daya daga cikin manyan masu sukar lamirin shugaba Muhammadu Buhari da gwamnatinsa, ya bayyana yadda shugaban kasar ya tarbe shi, yayin da aka gabatar masa da shi bayan sauya shekarsa.

Femi Fani-Kayode ya koma APC
Femi Fani-Kayode ya koma APC

Fani-Kayode ya wallafa a shafinsa na twitter a yau Juma’a cewa “Buhari ya bayyana matukar farin cikin matakin da na dauka na sauya shekar. Ya tarbe mu hannu bi-biyu, kuma mun tattauna sosai, inda na bayyana masa cewa na yanke shawarar komawa APC, kuma ya ji dadin wannan bayani.”

Shugaban rikon kwarya na jam’iyyar APC kuma gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ne dai ya gabatar da Fani-Kayode ga shugaban kasa, tare da rakiyar gwamnan jihar Zamfara Mohammed Bello Matawalle, bayan yanke shawarar komawa jama’iyyar APC.

Komawar ta shi a jam’iyyar ta APC mai mulki dai ya haifar da mabambantan ra’ayoyi a tsakanin ‘yan Najeriya, kasancewar yana daga cikin shahararren masu sukar gwamnatin Buhari a can baya.

XS
SM
MD
LG