A karshen taron da gwamnonin jihohin Arewacin Nigeria suka gudanar a Kaduna game da sake fasalin kasa, sunce zasu zagaya dukkan jihohin yankin don jin bukatar jama’a game da lamarin.
Da yake wa taron manema labarai bayani kan matsayin nasu, shugaban kwamitin Gwamnonin Arewacin Nigeria game da sake fasalin Nigeria, Gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal yace ba zasu fidda matsayar su ba sai bayan sun kammala jin abinda jama’arsu ke so.
Yace kwamiti nasa zai tattaro masana daga jihohi daban-daban domin duba wannan batu.
Haka kuma za a shirya tarurruka domin ‘yan arewanci su tofa albarkacin bakin su game da wannan batu.
Gwamnan na jihar Sokoto yace kwamitin nasa zai gudanar da wannan aiki mataki-mataki kafin Arewa ta fidda matsaya.
Sai dai a wuri daya kuma, matasan yankin sunce tuni aka wuce wannan wurin.
Ga Isah Lawal Ikara da Karin Bayani
Facebook Forum