Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gyauron ‘Yan Boko Haram ne Ke Kai Hare Hare A Najeriya, Inji Shelkwatar Soji


Harin Da Boko Haram Ta Kai Unguwar Jiddari-Pollo.
Harin Da Boko Haram Ta Kai Unguwar Jiddari-Pollo.

Rundunar tsaron Najeriya tace burbudin ‘yan Boko Haram ne da suka rage, suke kai ‘yan hare haren da ake gani a baya bayan nan.

Da yake jawabi ga manema labarai, darektan watsa labarai na rundunar Majo Janar John Enanche, ya bayyana cewa, suma ba wata babbar barazana bace, ya kuma bada tabbacin cewa, suma nan ba da dadewa ba za a shawo kansu.

Tun bayan kwace jejin Sambisa aka daina jin dakarun kasar suna kai hari kan kungiyar Boko Haram, amma a maimakon haka, sai kungiyar take kara zafafa kai hare hare..

Tsohon gwamnan mulkin soja a jihar Kano, majo janar Idris Garba mai ritaya wanda ya kasance masanin tsaro ya bayyana cewa, kungiyar bata da karfi yanzu sabili da an warwatsar da membobinta gaba daya.

A nasa bangaren Majo Janar Yakubu Usman wani babban jami’in soja a shelkwatar sojin Najeriya mai ritaya, ya bayyana cewa, kwace jejin Sambisa ba tare da an kashe Abubakar Shekau ba tamkar kashe maciji ne baka kashe kanshi ba, wanda zai iya samun karfi ya yi lahani.

Ga cikakken rahoton da wakilin Sashen Hausa Hassan Maina Kaina ya aiko daga birnin Tarayya Abuja.

Kara hare haren Boko Haram
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:39 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG