Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Boko Haram Na Yaudarar Matasa Da Gurguwar Fassara: Moussa Oumarou


Kamaru ta tura ministan tsaronta zuwa bakin iyakarta da Najeriya a can yankin arewacin kasar a bayan wasu hare-haren bam na kunar bakin wake da suka kashe mutane jiya jumma’a.

Hukumomi a Kamaru suka ce maharan sun kutsa cikin inda jama’a suka taru a kasuwanni da masallatai a yayin da ake kawo karshen azumin watan Ramadan.

Likitoci a asibitin garin Mora dake arewacin Kamaru sun ce sun duba mutane akalla 50, ciki har da wani jariri mai kwanaki 40 kacal da haihuwa, wadanda suka ji rauni a hare-haren bam har 6 da aka kai na kunar bakin wake a garuruwan Mora da Kolofata cikin ‘yan sa’o’i 24.

Gwamnan Jihar Arewa Mai Nisa, Mijinyawa Bakari, yace maharan su 6 matasa, cikinsu har da mata 3, sun shigo daga Najeriya domin kai hari kan inda mutane ke taruwa. Yace a cikin kwanaki goma da suka shige, hare-haren kunar bakin wake har guda 15 sun kasha mutane da dama a Mora da Kolofata.

Shugaban Kungiyar Limamai Musulmi ta Kamaru, Moussa Oumarou, yace sun tura wakilai domin janyo hankulan limamai na garuruwa da kauyuka kan yadda zasu kara sanya idanu da nufin rigakafin wannan. Yace ‘yan ta’addar suna yaudarar mutane, musamman matasan da hankulansu basu gama cika ba cewar wai idan suka mutu ta wannan hanyar zasu shiga aljanna, abinda yace gurguwar fassara ce.

A yau asabar, ministan tsaro, Joseph Beti Assomo, da manyan hafsoshin sojan kasar ta Kamaru sun doshi arewacin kasar domin karfafa tsaro a yayin da Musulmi ke shirin bukukuwan sallar azumi.

‘Yan Boko Haram da ake zargi da wadannan hare-haren sun yi sanadin mutuwar mutane akalla dubu 25, yayin da suka raba wasu mutanen fiye da miliyan 2 da dubu 700 da gidajensu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG