Shugaban Somaliland, Ahmed Mohammed Silanyo, shine ya gabatar da kudurin jiya Lahadi, a zaman hadin gwuiwar da majalisun duka biyu suka yi, yana mai cewa matakin "zai jawo masu zuba jari, kuma hakan bai zai jawo wata illa ga Somaliland ko yankin ba."
Wasu 'yan majalisar sun fusata wajen nuna adawa da kudurin, suna kalamai marasa dadi ga shugaban kasan , kamin a fidda su daga cikin majalisar. Daga bisani ne wakilai 144 cikin 151 dake majalisar suka amince da kudurin.
Idan har aka rattaba hannu kan yarjejeniyar, hakan zai baiwa hadaddiyar daular Larabawan madogara ta soji a yankin na kuryar Afirka. Tuni daular ta cimma irin wannan yarjejeniyar da kasar Eritrea.
Masu sharhi suka ce daular tana da niyyar kafa sansanonin sojin na lokaci mai tsawo, domin ta rika sa ido kan zirga zirgar ruwa a kuryar Afirka da kuma kogin Baharum ko Red Sea da turanci.