Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hadakar Jam'iyyun Adawa Ta Yi Alwashin Kada APC


PDP
PDP

Taron hadakar jam'iyyun adawar Najeriya 39 ya kammala da tsaida matsayar marawa 'yan takara na bai daya kama daga kan shugaban kasa zuwa kansila.

Babbar jam’iyyar adawa ta PDP, NCP ta marigayi Gani Fawehimmi, ADC da sauran su na cikin yarjejeniyar.


Dattawan siyasar arewa irin su Tanko Yakasai na kan gaba a taron da nuna gamsuwa ga hadakar.

"Kowane yunkuri kana yi masa kyakkyawan zato. Sai dai in kuma ka ga wani abu na gyara sai ka fada. Sai a yi fatan duk wanda yayi yunkurin yin wani abu, fatan Allah ya ba shi nasara," inji Yakasai.

Ya kara da cewa,

"Abin da na sani a siyasa ko ma a zaman duniya, mutane idan suka hadu sun fi karfi."

Sakataren kungiyar 'yan siyasar Arewa Dr.Umar Ardo ya ce duk jam'iyyun 39 dan takarar PDP za su marawa baya.


Taron dai ya kammala da kafa wakilai na taron jam'iyyun da za su rika zama don tsara muradin kawar da APC daga kan mulki a 2019.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:18 0:00

Facebook Forum

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG