Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hadakar kungiyar Filani Pulaku da gwamnatin Adamawa sun hada kai wajen yakar barayin shanu


Shanun sata da aka kwato
Shanun sata da aka kwato

Satar shanu a jihohin arewa ta zama tamkar ruwan dare gama gari musamman a jihohinarewa masu gabashin Najeriya inda jihar Adamawa take.

Hadin kan kungiyoyin makiyaya da gwamnatin Adamawa ya biyo bayan matsalar yawan satar shanu da kuma yin garkuwa da 'ya'yan Filani da yanzu suna neman su zama ruwan dare gama gari a wasu sassan jihar.

Kungiyar Filanin ta Pulaka tana nata kokarin gano 'ya'yansu ko kuma shanunsu da aka sace..Kungiyar tana gano wasu bata gari tare da sako wadanda aka yi garkuwa dasu ba tare da biyan kudin fansa ba.

Fulanin sun yi murna domin sun ce sun ga anfanin hadin kai na Tabital Pulaku . Suna shiga daji kuma har sun kwato yaransu sama da goma sha daya cikin sati biyu ba tare da biyan fansa ba.

Kugiyar Pulaku ta dade amma yanzu ta samu karbuwa ga wadanda can baya sun ki rungumarta.

Kungiyar ta soma sintiri a wasu kananan hukumomin jihar tare da jami'an tsaro.

Gwamnatin jihar Adamawa ta dauki alkawarin hadin kai da Pulaku domin yakar masu garkuwa da mutane da kuma satar shanu.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:19 0:00

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG