Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

HADARIN JIRGI: Shugaba Obama Ya Godewa 'Yan Kwana-kwana


Shugaban Amurka Barack Obama

'Yan kwana-kwana da suka ruga zuwa inda jirgin kasa ya samu hadari sun taimaka ainun wajen ceto rayuka da dama.

Shugaban Amurka Barack Obama yayimagana dangane da hadarin jirgin kasa da ya auku ranar Talata, inda ya godewa 'yan kwana-kwana, da wasu mutane da suka taimakawa wadanda hadarin ya rutsa dasu. Daga nan yayi kira kan bukatar ta kashe kudi wajen inganta kayan more rayuwa.

Da yake magana bayan kammala taron koli a gandun shakatawa na shugaban Amurka da ake kira Camp David dake jihar Maryland, Mr. Obama ya bayyana godiya ga 'yan kwana-kwana wadanda suka sheka zuwa inda aka yi hadarin domin su ceci rayuka, da kuma wasu fasinjoji masu yawa wadanda duk da irin raunuka da suka samu suka taimaka wajen tsirar da wasu fasinojin a inda jirgin kasa na fasinja da ake kira Amtrak yayi hadari a Philadelphia.

Haka nan shugaba Obama yayi ta'aziyya ga iyalan wadanda hadarin ya rutsa dasu.

An gano gawar wani fasinja daga cikin baraguzan jirgin jiya Alhamis, wanda yanzu ya kawo adadin wadanda suka mutu zuwa takwas, wasu mutum metan kuma suka jikkata, wasu raunukan nasu masu tsanani ne.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG