Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hadarin Jirgin Sama A Pakistan Ya Rutsa da Mutane 47


Wadanda suka rasa 'yanuwa a hadarin suna juyayi.

Wani jirgin saman Pakistan ya fadi a kan hanyarsa daga garin Chitral dake arewacin kasar zuwa Islamabad a jiya Laraba ya hallaka mutane 47 da suke cikinsa.

Jirgin mai lamba 661 na kasar ta Pakistan dake aiki zuwa kasa da kasa wato PIA ya yi kasa ne a wani yanki da tsaunuka da yawan gaske kusa da garin Havelian kafin ya kama da wuta a cewar shedun gani da ido da kuma yan sandan gundumar.

Pasinjoji 42 da ma’aikatar jirgin biyar ne ke cikin wannan jirgi kirar ATR-42. An riga an samu gawarwakin pasinjojin.

A cewar shedun gani da idon, galibin gwarwakin sun kone kurmus har ba a iya ganesu, sai dai hukumomi na gudanar da binciken kwayar halitta don ganosu kafin a mikasu ga iyalansu.

Wani kakakin soji yace jirgi mai saukar ungulu na rundunarsa shine ya taimaka wurin aikin ceton.

XS
SM
MD
LG