Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hadarin "Luxury Bus" A New York Ya Kashe Mutane 14


Wata Motar 'yan yawon bude ido da ta yi hatsari a birnin New York.

Hukumomin Amurka sun ce mutane 14 suka mutu sakamakon hadarin wata motar ‘yan yawon shakatawa a safiyar jiya Asabar,bayan da motar ta kara da wata babbar gofa karfe.

Hukumomin Amurka sun ce mutane 14 suka mutu sakamakon hadarin wata motar ‘yan yawon shakatawa a safiyar jiya Asabar,bayan da motar ta kara da wata babbar gofa karfe.

Mutum na 14 a Asibiti ya mutune.

‘Yansanda suka ce matukin motar yace wata trailer ce ta buga motar daga baya.Babu abinda ya sami gofar sai dai ta nemi raba motar gida biyu.

‘Yansanda suna neman matukin tralan d a ake zargin,wanda bai tsaya ba bayan da hadarin ya auku. Dukkan fasinjoji da suka tsira da ransu daga hadarin sun jikkata.

Bas din dake dauke da fasinjoji 32 tana kan hanyar dawowa birnin New York ne bayan ziyara da suka kai wani wurin tambola dake jihar Connecticut makwabciya.

Ahalin yanzu kuma wata Bus ta yi hadari a kasar Haiti ta kashe mutane tara ta jikkata wasu 24.

XS
SM
MD
LG