Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hadarin Mota Tsakanin Bauchi da Ningi Ya Rutsa da Rayuka 12


Gwamnan Jihar Bauchi, Barrister M.A. Abubakar

Wata mota dauke da 'yan banga tayi taho mu gama da motar tankar mai tsakanin Bauchi da Ningi wanda ya yi sanadiyar mutuwar 'yan bangan goma sha biyu

Jiya Alhamis da misalin karfe uku na rana motar wasu 'yan banga tayi taho mu gama da motar tankar man fetur a kauyen Kafin Liman inda rayuka goma sha biyu suka salwanta.

Baicin wadanda suka mutu akwai wasu kuma da suka samu munanan raunuka wadanda 'yansanda suka ruga dasu asibiti domin samun jinya.

Irin hadarin da tukin ganganci kan jawowa al'umma
Irin hadarin da tukin ganganci kan jawowa al'umma

Cikin wadanda suka rigamu gidan gaskiya goma sha daya 'yan banga ne kana mutum daya shi ne direban tankar mai din da suka yi hadari tare.

Mai magana da yawun 'yansanda yace ita tankar mai din babu mai a cikinta, lamarin da watakila shi ya sa take mugun gudu.

Su 'yan banaga din sun fito ne daga Ningi suna komawa Bauchi suka hadu da ajalinsu a Kafin Liman.

Hadarin ya baza baraguzen motocin a kan hanya har sai da aka rufe hanyar na wani dan lokaci kafin 'yansanda su kawar dasu a bar motoci su cigaba da wucewa.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:43 0:00
Shiga Kai Tsaye

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG