Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hadin Kan Najeriya Na Fuskantar Babbar Barazana – Bukola Saraki


Tsohon mshugaban majalisar dattawa, Dr. Bukola Saraki.

Tsohon shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Dr. Bukola Saraki ya nuna damuwarsa kan rikicin makiyaya da manoma da ke wakana a jihohin Ondo da Oyo lamarin da har ya kai ga aka ba Fulanin wa’adin su tashi a wasu yankunan jihar ta Oyo.

Cikin wani dogon sakon Twitter da ya wallafa a shafinsa, Saraki ya ce wannan al’amari ya kara zaman dardar da ake yi a Najeriya.

“Wannan mummunan al’amari da ke faruwa a wadannan jihohi biyu, alamu ne da ke barazana ga hadin kan kasarmu kamar yadda muka gani abin yake faruwa a wasu sassan kasar nan.”

Saraki ya kuma yi kira ga "kowa da kowa" da ya dukufa wajen tabbatar da zaman lafiya tare da daukan matakan da za su kwantar da hankula.

“Shirun da masu ruwa da tsaki, da shugabannin suka yi a wannan lamari, wadanda ya kamata a ce sun yi magana, abin damuwa ne. Wannan alama ce da ke nuna akwai damuwa. Wannan shiru ba alheri ba ne ga kasarmu.”

“Ina kira ga shugaba Muhammadu Buhari, da ya shige gaba a wannan al’amari, ka dauki matakin da kowa zai san cewa kana kokarin shawo kan wannan matsala.”

Ya kuma kara da cewa, “wannan lokaci da kowa da kowa ya kamata ya kawo tasa gudunmowar. Wannan ba lokaci ba ne na magana akan APC ko PDP. Lokaci ne da kowa zai yi wa Najeriya aiki.”

A cewar Saraki, “wannan ba lokaci ba ne na zama ana zira ido ana kallo, ana jiran zabe na gaba ya zo, muna daukan alkawura wanda hakan bai za taimaki kowa ba. Wane irin zabe za mu yi a shekarar 2023 idan al’amura suka ci gaba da tafiya a haka? Rigaki ya fi magani.”

A ‘yan kwanakin nan an samu matsala tsakanin makiyaya Fulani da manoma a yankunan jihar Ondo da Oyo lamarin da ya kai ga asarar rayuka.

Mazauna jihohin suna zargin Fulanin da aikata ayyukan da ke barazana ga tsaro, abin da shugabannin Fulani suka musanta.

Rahotanni da dama sun nuna cewa wani hari da aka kai rugagen Fulani ya haddasa asarar rayukan da dama a wani kokari da al’umar yankin ke yi na korar Fulanin daga yankin.

XS
SM
MD
LG