Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Halin Da Gwamnan Bauchi Ke Ciki Bayan Kamuwa Da Coronavirus


Gwamnan Bauchi Bala Mohammed
Gwamnan Bauchi Bala Mohammed

Bayan da aka fitar da sanarwar cewa gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad ya kamu da cutar coronavirus, kwamishinan lafiya na jihar ya yi wa Muryar Amurka karin bayani kan halin da gwamnan ke ciki.

A cewar Dr. Aliyu Maigoro, gwamnan yana nan a killace inda ake ba shi magunguna.

“Cibiyar dakile cututuka ta NCDC ta turo ma’aikatanta cikin jirgi domin su zo su taimaka mana, kuma su koya wa ma’aikatanmu da ke nan yadda za a kula da masu cutar,” in ji kwamishinan.

Ya ce gwamnan yana nan cikin koshin lafiya, ba tare da wani ciwo ba, kuma ba wanda ke zuwa wajensa sai dai likitan da ke kula da shi.

Ya kuma kara da cewa “an yi gwajin cutar kan fiye da mutum 15 da ake ganin cewa sun yi mu’amala da shi, su kuwa iyalansa an killace su su ma.”

Ya zuwa yanzu dai mutum 44 ne ke dauke da wannan cutar ta Coronavirus a Najeriya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG