Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Halin Sadaukar wa Ne Ke Sa Kasa Ta Ci Gaba – Buhari


Muhammadu Buhari

Idan har ana bukatar kasa ta ci gaba, dole ne sai al'ummar wannan kasa ta nuna hali na sadaukar da rayuwa ta jin dadi a wasu lokuta kafin a cimma wannan buri, a cewar shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya ce, har sai al’umar kasar musamman masu hanu da shuni, sun nuna hali na sadaukar wa kafin kasa ta ci gaba.

“A halin da Najeriya ke ciki yanzu, akwai bukatar kowa da kowa ya nuna hali na sadaukar wa idan har muna so mu magance matsalolin cin hanci da talauci da aikata manyan laifuka da kuma rashin ci gaban da muke fuskanta.” Inji shugaba Buhari.

Buhari ya bayyana hakan ne, yayin da yake ganawa da wasu shugabannin jihar Katsina a Daura, kamar yadda wata sanarwa da mai bai wa shugaba Buhari shawara kan harkar yada labarai, Malam Garba Shehu, ya saka wa hannu wacce Muryar Amurka ta samu.

Sanarwar ta kara da cewa, shugaba Buhari ya jaddada cewa “akwai lokutan da dole sai al’umar kasa ta sadaukar da rayuwa ta jin dadi” kafin kasa ta ci gaba.

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Masari ne ya jagoranci tawagar shugabannin jihar zuwa Birnin na Daura, domin su yi wa Buhari ta'aziyyar bisa rashin wasu ‘yan uwansa da aka yi.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG