Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hambararren Shugaban Masar Mohammed Morsi Ya Rasu


Tsohon shugaban Masar. Mohammed Morsi
Tsohon shugaban Masar. Mohammed Morsi

A shekarar 2013, sojoji suka kifar da gwamnatin Morsi, wanda shi ne shugaban kasar Masar na farko da aka zaba karkashin mulkin Dimokradiyya, bayan zanga zangar adawa da salon mulkinsa.

Tsohon shugaban kasar Masar Mohammed Morsi da aka kifar da gwamnatinsa ya rasu a yau Litinin.

Ya rasu yana da shekaru 67.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa, Morsi ya yanke jiki ya fadi ne bayan wani zaman kotu da aka yi a yau, inda daga baya kuma ya cika.

A shekarar 2013, sojoji suka kifar da gwamnatinsa, wanda shi ne shugaban kasar Masar na farko da aka zaba karkashin mulkin dimokradiyya, bayan zanga zangar adawa da salon mulkinsa.

Ya kasance jigo a kungiyar ‘yan uwa musulmi ta Muslim brotherhood.

An zabe shi ne a shekarar 2012 bayan juyin-juya halin da ya faru a wasu kasashen larabawa a shekarar 2011, wanda ya yi sandin kawar da gwamnatin Hosni Mubarak.

Morsi na tsare ne saboda yana fuskantar tuhuma bisa zargin hada kai da kungiyar Hamaz.

An haramta kungiyarsa ta Muslim Bortherhood a kasar ta Masar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG