Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Marigayi Homun Stephen Ya Taka Rawa Wajen Samar Da Zaman Lafiya a Adamawa


Marigayi Homun Stephen
Marigayi Homun Stephen

A yayin da ake ci gaba da alhini da kuma jimamin rashin da aka yi na babban basaraken kabilar Bachama da ke jihar Adamawa wato Homun Honest Stephen, yanzu hankula sun karkata ga batun wanda zai maye gurbinsa ganin irin rawar da ya taka wajen samar da zaman lafiya a lokacin da ya ke kan karagar mulki tsawon shekaru takwas.

Shi dai marigayi Homun Stephen wanda tsohon kanar din soja ne, tuni aka yi Jana’izarsa a ranar Lahadi 28 ga watan Yuni a garin Lamurde kamar yadda al’adar Bachama ta tanadar, ya kuma rasu yana da shekaru 66 a duniya.

A shekarar 2012 ya fara mulki a zamanin gwamnatin Murtala Nyako, ya kuma karbi sarautar ne biyo bayan rasuwar marigayi Homun Asaph Zadok, wanda ya rasu a birnin Alkahira bayan fama da jinya.

Chief Timawus Mathias, da ke zama Nzobyalata Hama Bachama, Kuma Mai magana da yawun masarautar ya ce za a dade ana tuna rawar da marigayi Homun Honest Stephen ya taka a zamaninsa.

A sakon jaje da ya aika wa gwamnati da kuma al’ummar jihar Adamawa, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a ta bakin hadiminsa ta fuskar harkokin yada labarai Mallam Garba Shehu, ya bukaci masarautar Bachama ta yi karatun ta natsu wajen nadin sabon sarkin da zai dora kan abun da ya kira “kyawawan ayyukan” marigayi Homun Honest Stephen.

Saurari karin bayani cikin sauti.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG