Kasar Kamaru ta ce matakan gwaji da sa ido da aka dauka a kasar dake tsakiyar Afrika tun bayan da aka samu rahotannin bullar cutar a China sun taimaka wajen tabbatar da mutumin da ya shiga Kamaru da cutar ranar Juma’a. Jami’ai sun ce wani dan kasar Faransa da ya isa kasar ranar 24 ga watan Fabarairu ne ya shigo da cutar.
Ministan harkokin lafiyar Kamaru Manaouda Malachie ya ce ba tare da bata lokaci ba, an killace mutumin dan Faransa mai shekara 58 da haihuwa a wani asibitin kwararru dake birnin Yaounde bayan da aka yi tunanin yana dauke da cutar. Malachies ya kuma yi kira ga ‘yan kasar akan su kwantar da hankalin su, ya kuma ce an horar da jami’an kiwon lafiya akan yadda zasu tunkari cutar.
Wannan labarin bullar cutar ya tada hankalin ‘yan Kamaru sosai da ya sa da dama suka rika zuwa asibiti da shagunan saida magani don neman shawara.