Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hannun Agogo Ya Koma Baya a Isra'illa Inda Aka Kara Saka Matakan Kulle


Frai Minista Benjamin Netanyahu
Frai Minista Benjamin Netanyahu

Kasar Isra'illa ta sake kakkaba wasu sabbin matakai bayan da adadin masu kamuwa da Coronavirus a kasar ya karu.

A cewar gidan rediyon Israel Radio, gwamnati ta umarci da a rufe wuraren motsa jiki da gidajen bukukuwa da gidajen shan barasa.

Yadda wasu mutane suke rawa bayan da aka cire wasu matakan kulle a Isra'illa a kwanakin baya
Yadda wasu mutane suke rawa bayan da aka cire wasu matakan kulle a Isra'illa a kwanakin baya

A yayin wani taro inda aka yanke wannan hukuncin, fraim ministan kasar Benjamin Netanyahu ya ce dole sai Isra'illa ta kara kakkaba wasu matakai domin takaita yadda cutar ke kara yaduwa.

Ya zuwa yanzu Isra'illa na da fiye da mutum 30,000 wadanda cutar ta Covid-19 ta harba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG