Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Har Yanzu An Kasa Kashe Gobarar Da Ke Ci a California


Wutar daji na ci a jihar California
Wutar daji na ci a jihar California

A yau Laraba hukumomi sun yi gargadin cewa gobarar dajin da aka kasa shawo kanta na can na ci a jihar California, kuma ta yiwu iska ta kara tsananta gobarar.  

Masana sun yi hasashen cewa za a samu iskar Diablo da ke kadawa daga arewacin jihar da kuma iskar Santa Ana daga kudanci a yau Laraba 9 ga watan Satumba a lokacin da gobarar da ke ci ke kara tsananta.

A jiya Talata, a kan dole jami’an kwana-kwana 14 suka kafa sansanonin gaggawa yayin da gobarar ta sha gabansu ta kuma ta lalata cibiyar yankin Nacimiento, wata cibiya ta ‘yan kwana-kwana da ke dajin Los Padres na Kasa a gabar tekun da ke tsakiyar jihar.

Yadda wani mai aikin kashe gobara ke hutawa bayan aiki
Yadda wani mai aikin kashe gobara ke hutawa bayan aiki

Jami’an sun samu raunuka sun kuma shaki hayaki, sannan uku daga cikinsu an kai su wani asibiti a Fresno, kuma ɗaya daga cikinsu na cikin mawuyacin hali.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG