Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Har Yanzu Ana Fama Da Wahalar Buga Wayoyi A Arewa Maso Gabashin Najeriya


Wani mutum na amfani da wayarsa samfurin Blackberry a Najeriya.
Wani mutum na amfani da wayarsa samfurin Blackberry a Najeriya.

I yanzu dai, mutane da yawa basu san halin da ‘yan uwansu suke ciki ba a jihohin arewa maso gabashin Najeriya da aka kaddamar musu da dokar ta baci.

“Wannan lamba da kuka buga bata samuwa, a sake gwada lamba idan an dan juma.” Wannan itace kashedin da jama’a suke ji idan sunyi kokarin buga waya zuwa wasu sassan jihohin Najeriya uku da aka kaddamar musu da dokar ta baci.

Wadannan jihohi sune Borno, Yobe da Adamawa, kuma yau kwanaki 10 tun bayan kaddamar da dokar, kuma hakan ya zone da da katsewar duka hanyoyin sadarwa ta wayar tarho a mafi yawancin wadannan jihohi.

Dakarun Najeriya sun katse layukan wayoyin ne domin kaddamar da hare-hare kan ‘yan kungiyar nan ta Jama’atu Ahlil Sunna Li Da’awa wa Jihad da ake kira Boko Haram.

An Katse layukan wayoyin ne bayan da dakarun Najeriya suka fara isa yankunan arewa maso gabashin Najeriya dake kusa da kasar Nijar, Kamaru da Cadi.

A dai-dai lokacin da dakarun Najeriya ke yunkurin kwato wasu sassan jihohin Borno, Yobe da Adamawa, jin ta bakin wasu daga cikin mutanen wadannan jihohi yayi wahala, kuma ma wasu mutanen kamar wani mutum da baya so a fadi sunansa.

“Tun tahowa na daga Damaturu, ina ta neman wayan iyalaina, ban same su ba, ina ta neman wayan abokaina da sauran ‘yan uwana.” Inji wannan mutum kennan da yake ganawa da wakilin Muryar Amurka Abdulwahab Mohammed.

Wani manomi kuwa, ya alaqanta katse layukan waya da zalunci. A ganinshi, hanya ce da dakarun Najeriyan ke amfani da ita wajen cin karensu babu babbaka.

Jihar Borno itace tungar kungiyar da ake kira Boko Haram, kuma anan ne aka fara wannan rigima tun shekara ta 2009 bayan da ‘yan sandan Najeriya suka kashe wasu ‘ya’yan kungiyar, da shugaban kungiyar Muhammad Yusuf a fili ba tare da shari’a ba. Wannan ya fusata kungiyar, shine suka dauki makamai suka fara kaiwa dakarun tsaro, sojoji da gidajen Yari hari a duk fadin arewacin Najeriya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:49 0:00
Shiga Kai Tsaye
Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG