Accessibility links

Idan ba'a manta ba ranar Litinin da ta gabata wasu 'yan bindiga suka kai hari akan kasuwar garin Gamborun Ngala da ma garin inda suka kashe mutane fiye da dari uku. Amma kuma kawo yanzu ana cigaba da zakulo gawarwaki daga shaguna inda suka kone.

Garin Gamborun Ngala yana kan iyaka ne da kasar Kamaru kuma yana da tazarar kilomita dari da talatin da biyar daga Maiduguri babban birnin jihar Borno.

Kawo yanzu dai alamura sun tsaya cik a garin Gamborun Ngala domin gidaje fiye da dari aka kone haka ma kasuwar baki dayanta aka kone. Duk wani wurin kasuwanci a garin an koneshi. Bugu da kari ana cigaba da zakulo gawarwakin wasu da wuta ta rutsa dasu a cikin shagunansu yayin da maharan suka farma kasuwar.

Mutanen garin da suka tsira suna cigaba da zaman juyayi da alhini game da abun da ya addabesu. Abdulrahaman Terab dan majalisa mai wakiltar shiyar ya yiwa wakilin Muryar Amurka karin bayani. Yace abun da suka fuskanta babu irinsa da ya taba faruwa a yankinsu. Yace yau an wayi gari dan kasuwa komi kankantansa bashi da jari ko na sisin kwabo. Wannan lamarin bala'i ne. A ganinsa rayukan da aka yi asara sun fi dari uku.

Lokacin da suka kai ziyara cikin kasuwar tana cigaba da konewa. Akwai wasu shaguna da an kasa shiga cikinsu domin sun rikito akan mutane. Akwai gawarwaki da dama da suke cin wuta. Motocin tiriloli da aka bankawa wuta har yanzu wuta tana ci akansu. Tirilolin da aka kona sun fi talatin.

Dan majalisar yace idan ba'a nemi tushen matsalar ba to za'a cigaba da zama cikin bala'i. Kamata yayi a yi gaskiya a nemi dalilin da yasa aka shiga irin wadannan halayen. A ganinsa yace wani irin shiri ne na karya tattalin arzikin arewa musamman jihar Borno.

Lokacin ziyarar motoci sama da dari uku da saba'in aka gani an konasu. Mutanen garin Gamborun Ngala suna cikin wani mawuyacin hali domin yayin da aka kai harin yara maharan suka jera suka fara harbinsu daya bayan daya duk da ba wani laifi suka yi ba.

Muhammed Abubakar Bishara shugaban masu manyan motoci yace harin ya fi shafar 'ya'yan kungiyarsu domin ya rutsa da 'ya'yan kungiyar da dama da kuma dukiyoyinsu. Yace babbar mota daya mutanen dake cin abinci karkashinta sun fi hamsin. Yace lamarin ya wuce tunane. Yana bukatar addu'a da kulawa kada ya kara tabarbarewa. Yace a dauki duk matakan da za'a iya dauka wajen magance matsalar.

Ga rahoton Haruna Dauda Biu.
XS
SM
MD
LG