Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Har Yanzu Ba A Ceto Mahaifiyar Mataimakin Gwamnan Taraba Ba


Yan Sandan Najeriya.

Kamar yadda rahotanni ke nunawa zuwa yanzu ba’a ceto mahaifiyar mataimakin gwamnan jihar Taraba,Haruna Manu da wasu yan bindiga suka sace a garin mutum biyu,wanda yanzu haka ba’a san halin da take ciki ba.

Yanzu haka dai Jami’an tsaro da kusoshin gwamnatin jihar Taraba ne ke kokarin ganin an ceto mahaifiyar mataimakin gwamnan jihar, Hon. Haruna Manu, Hajiya Hauwa da ake yiwa lakabi da Hajiya Beli, wadda wasu ‘yan bindiga suka sace a garin Mutum-Biyu hedikwatar karamar hukumar Gasol.

Yanzu haka dai al’umar garin na cikin wani al-hini, yayin da rahotanni ke cewa maharan na neman a basu kudin fansa na kusan Naira MIliyan dari uku. Wasu daga cikin mutanen dake gidan Hajiya Beli, alokacin da lamarin ya faru sun bayyanawa wakilin Muryar Amurka yadda abin ya faru.

Inda suka ce mahara biyu ne dauke da bindigogi suka suka shiga gidan suka kama Hajiya Beli, daga baya kuma suka harbe wani dan kasuwa mai suna Mallam Usaini Kano, da suka zargi ya kawo dauki ne acewar mahaifinsa.

Wani dan uwan mahaifiyar mataimakin gwamnan ya mika kokon bararsu ga maharan da ke garkuwa da ita, yana mai cewa yiwa Allah su taimaka domin a halin da take ciki yanzu bata da lafiya, su taimaka su sake ta.

Don karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:51 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG