Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Har Yanzu Bazoum Ne Shugaban Nijar – Amurka


Biden
Biden

Ganawar ta Blinken da Bazoum na zuwa ne yayin da sojojin da suka yi juyin mulki suka nada gwamnoni a jihohi takwas da ke kasar.

Sakataren harkokin Wajen Amurka Antony Blinken, ya ce har yanzu Amurka na ci gaba da nuna goyon bayan Shugaba Mohamed Bazoum da sojojin kasar suka hambarar a makon da ya gabata.

Blinken ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da ya yi da Bazoum ta wayar tarho a ranar Laraba kamar yadda sanarwar da ofishinsa ta fitar ta nuna.

A makon da ya gabata sojojin da ke tsaron fadar shugaban kasar ta Nijar karkashin Janar Abdourahame Tchinia suka tsare Bazoum suka kuma ayyana juyin mulki, lamarin da kasashen duniya da dama suka yi Allah wadai da shi.

“Sakatare Blinken ya jaddawa Bazoum ci gaban goyon bayan Amurka da tsarin dimokradiyyar Nijar.

“Ya kuma kara jaddada cewa Amurka na tir da kifar da tsarin na dimokradiyya, ya kuma nuna cewa yana tare da al’umar Nijar da ECOWAS da AU da sauran kawayen kasashe da ke goyon bayan mulkin dimokradiyya da mutunta tsarin doka da kare hakkin bil adama.” Sanarwar ta ce.

Ganawar ta Blinken da Bazoum na zuwa ne yayin da sojojin suka nada gwamnoni a jihohi takwas da ke kasar, wani abu da masu lura da al’amura suka ce yunkuri ne da sojojin suke yi na kara damke mulki.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG