Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Har Yanzu Janaral Aliyu Gusau ne Ministan Tsaron Najeriya


Janaral Aliyu Gusau Ministan Tsaro Najeriya
Janaral Aliyu Gusau Ministan Tsaro Najeriya

Kwanan nan kafofin labaran yanar gizo suka yayata wata jita-jita cewa ministan tsaron Najeriya Janaral Aliyu Gusau ya yi murabus bisa ga wasu dalilai

Kodayake raderadin cewa Janaral Aliyu Gusau ya yi murabus na cigaba da yaduwa amma kawo yanzu shi ministan bai fito fili ya fadi hakan ba kuma gwamnatin tarayya bata ce komi ba game da lamarin.

To amma sabili da kafofin labarai ta yanar gizo sun yayata batun da wuya a kankare maganar daga zukatan 'yan Najeriya musamman wadanda suka dogara da wayar tafi da gidanka da samun labarai.

Idan ba'a manta ba lokacin da majalisar dattawa ke tantance sunayen sabbin ministocin da shugaban kasa ya mika, shugaban majalisar Sanata David Mark bai ma bari an yiwa Janaral Aliyu Gusau wata tambaya ba. Cewa yayi ya tafi abinsa domin gamsuwa da cancantarsa na rike mukamin ministan tsaro. 'Yan majalisar sun yi la'akari da irin kwarewarsa da jajewarsa kan aikin tsaro musamman a lokutan baya. Mutum ne da kasar gaba daya ta ga irin kamun ludayinsa a harkokin tsaro da makamantansu.

Shettiman Rijiya Faruk Gusau yace basu goyi bayan jita-jitar ba domin sun san ya san aikin da aka bashi yayi kuma yana iya yin irinsa koina. Ya kara da cewa zai iya wakiltar jihar Zamfara. Yace sabili da haka ba zasu yadda da jita-jita ba domin haka ya yi watsi da ita.

Useni Mongunu wani masani kan harkokin tsaro yana ganin ta yiwu an ki cika wasu sharuda da shi Janaral Gusau ya shimfida kafin karbar aikin. Yace dattijo ne kuma a harkar tsaro ya dade yana aikin. Tun kafin ya fara aikin ya riga ya fadama gwamnati abubuwan da yake so ya gani da irin mutanen da zai iya aiki dasu.

Ga karin bayani.
XS
SM
MD
LG