Accessibility links

Gaskiya ne General Aliyu Gusau Yayi Murabus Daga Matsayin Ministan Tsaro?

  • Aliyu Mustapha

General Aliyu Gusau

Sabon ministan tsaro na Nigeria General Aliyu Gusau ya maida murtani ga rahottanin cewa yayi murabus

Sabon ministan tsaron Nigeria General Aliyu Mohammed Gusau yace ba gaskiya bane, labaran da wasu kafafen yada labarai na duniyar gizo (Internet) suka bada na cewa wai ya sauka daga mukaminsa. A cewar rahottanin, General Gusau ya sauka ne saboda wata rashin jituwar da tashiga tsakaninsa da manyan hafsoshin sojan Nigeria. Amma a hirarsa da Sashen Hausa na VOA, General Gusau yace labarin ba gaskiya bane, yana nan kan mukaminsa. Duk da haka wakilin Sashen Hausa na VOA Abuja Nasiru Adamu El-Hikaya ya gayawa Bello Galadanchi sarsalar inda wannan labarin uya samo asali:

XS
SM
MD
LG