Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Har Yanzu Mata Na Fama Da Koma Baya A Fanonnin Rayuwa Daban Daban - Matan Najeriya


Yadda gidan talbijin na Arewa 24 ya gudanar da bikin ranar mata ta duniya (Hoto: Facebook/Dinat Dama Maji)
Yadda gidan talbijin na Arewa 24 ya gudanar da bikin ranar mata ta duniya (Hoto: Facebook/Dinat Dama Maji)

A yayın da ake bukin Ranar Mata ta Duniya a yau Juma’a 8 ga watan Maris na shekarar 2024, wanda aka yiwa taken Zuba jari ga mata: Habaka ci gaba, dubban mata na jan hankali a kan yiyuwar jefa Mata miliyan 340 a duniya cikin tsananin talauci idan ba’a dauki matakan da suka dace cikin gaggawa ba.

ABUJA, NAJERIYA - A yanayin da ake ci a yanzu, duniya na fuskantar rikice-rikice da yawa, kama daga na yanki-yanki, kasa da kasa, zuwa ga matsalolin matsanancin talauci, yunwa, tsadar rayuwa, tashin farashin kayayyakin abinci masu alaka da matsin tattalin arziki da karuwar tasirin sauyin yanayi.

Masu fafutukar neman an baiwa mata damammaki kamar takwarorinsu maza sun bayyana cewa za a iya magance waɗannan ƙalubalen ta hanyar matakan ƙarfafa mata, saka jari ga ci gaba mata, don su iya jagorantan sauyi cikin aminci da daidaito a duniya ga kowa.

Shin ina aka kwana a game da baiwa mata damammakin da suka dace kamar yadda ake fifita takwarorinsu maza, kwararriya a fannin sadarwa, Ambassada Khadija Ishaq Bawas, ta ce a wasu kasashen duniya da suka ci gaba Ana asasa wannan taken na shigar da mata a dama da su, saidai a cikin gida wato Najeriya da saura rina a kaba.

A nata bangare, ‘yar siyasa kuma mai fafutukar ganin an shigar da mata fannin da Saura muhimman fanonnin rayuwa, Onarable Zainab Buba Galadima ta bayyana cewa ganin alkalumma da suka yi nuni da cewa idan ba’a dauki matakan da suka dace cikin gaggawa ba mata miliyan 342 zasu fada cikin tsananin talauci har yanzu ana rarrafe ba’a kai ga daukan mataki ba.

Saidai kwararriya a fannin tattara haraji kuma yar kasuwa malama Binta Gaude ta na mai ra’ayin cewa gaskiya mata sun sami ci gaba a fanonni da dama duk da cewa ba’a kai ga inda ake so ba.

Alkaluman kididdiga sun yi nuni da cewa da saura aiki a fannin ci gaban mata musamman ganin yadda akwai gibi a fannin basu damar su yi mulkin siyasa, jagoranci cibiyoyi ko kamfanoni masu zaman kansu lamarin da masu fafutuka suka ce abun a sake dubawa ne don ci gaba a duniya baki daya.

Har Yanzu Mata Na Fama Da Koma Baya A Fanonnin Rayuwa Daban Daban - Matan Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:59 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG