Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Har yanzu Sojoji ke Rike da Garin Bama

Bayan harin da ake kyautata cewa ‘yan Boko Haram ne suka kai garin Bama a jiya, wanda ya dagulawa garin lissafi, wani sabon alamura ne ke kuno kai, na karyata wannan batu na cewa ‘yan kungiyar Boko Haram ne ke rike da garin Bama.

A wani taron manema labarai da kungiyar civilian JTF suka kira yau a garin Maiduguri, sun ce ba gaskiya bane furushi da akeyi cewa ‘yan Boko Haram, sun karbe shugabancin ragamar garin, da kuma barikin sojoji dake cikin garin Bama.

Tun a jiya ne dai aka dinga ganin mutane da dama masamman mata da yara na kwararowa cikin Maiduguri, daga garin Bama sakamakon karan harbe-harbe bidiogogi.

Sai dai kawo yanzu babu wani jawabi daga hukumomin tsaro, game da wannan nasarori da aka samu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG