Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Malaman Makaranta Sun Damu akan Rufe Makarantunsu


Yara 'Yan Makaranta.

Ma’aikatan ilmi a Najeriya sun nuna damuwarsu akan yanda gwabnatin ta kara wa yara ‘yan makaranta hutu domin fargabar yaduwar cutar Ebola a Najeriya.

Ma’aikatan ilmi a Najeriya sun nuna damuwarsu akan yanda gwabnatin ta kara wa yara ‘yan makaranta hutu domin fargabar yaduwar cutar Ebola a Najeriya. Wadda take cutace guda daya tak, shin ko ina gabnatin Najeriya take alokacin da ake kashe da sace ‘yan makaranta acikin gidajensu da kuma a makarantarsu, meyasa baza’a tsayar da karatu ba a wannan lokacin? Yanzu kawai don cuta daya sai a rufe makarantu.

Yawancin ‘yan makarantar suna cikin hutu ne, kuma zasu koma sati maizuwa, to shine ma’aikatan gwabnati sukayi sanarwa da cewa za’a koma 13 ga watan October.

Wasu daga cikin iyayen yaran sun nuna damuwarsu akan al’amarin, haka kuma wasu daga cikin ma’aikatan makarantar suma sun nuna tasu damuwar.

Sama da mutane dubu daya da dari hudu sun mutu daga cutar Ebola a yammacin Afirka, mutum biyar daga ciki ne ‘yan Najeriya amma duk da haka mutane na nuna damuwarsu cewa cutar zata iya barzama idan har ba’a doki mataki ba.

Babbar matsalolin da makarantun Najeriya zasu shiga sune rashin kulawa da rashin tsaro. Ana jan makarantunne akasa saboda rashin ishashshun kayan aiki, da kuma barin malaman makaranta sutafi yajin aiki da rashin kulawa da kasancewar ‘dalibai suna zuwa makaranta.

‘Yan Boko Haram sunkashe yara dayawa sunkuma kame wasu yaran dayawa, harma sun janyo wa’yansu iyayen yara sun hana ‘ya’yan su zuwa makaranta. Amma ina gwabnati take alokacin da ake bukatarta, duk wannan bai sa an rufe makarantu ba saida wanna cutar Ebola ta zo.

Najeriyar de tace suna fatan wannan cutar Ebola zata bar kasar Najeriya gabadaya daga nan zuwa cikin watan satumba ta wannan shekarar, kuma sunce haryanzu suna kan bakarsu ta ganin haka ya tabbata. Yadda karuwar yaduwar cutar ke bazama a cikin yammacin Africa, haryanzu cutar na kara karuwa a Guinea, Sierra Leone da kuma Liberia. Amma haryanzu cutar na barazanar yaduwa a Najeriya da sauran nahiyar ta Africa.

XS
SM
MD
LG