Accessibility links

Duk da matakan sojan da gwamnati take dauka na murkushe Boko Haram, har yanzu babu alamar al'ummar arewa maso gabashin Najeriya zasu samu kwanciyar hankali.

Har yanzu tashin hankali bai kare a yankin arewa maso gabashin Najeriya ba, duk da matakam da sojoji suke dauka na murkushe Boko Haram. Jami'an gwamnati suka ce duk da cewa an samu korar 'yan bindigar daga cikin manyan garuruwa, har yanzu su na kai hare-hare a yankunan karkara.

Wasu 'yan Najeriya ma su na fargabar cewa a yanzu 'yan bindigar sun fara fita zuwa jihohin da babu dokar-ta-baci.

A wannan makon a Jihar Bauchi, wadda ba ta cikin jihohi ukun da aka kafa dokar-ta-baci, an kashe 'yan sanda hudu, aka ji rauni ma wasu 2 a musanyar wuta daren alhamis. Wani shaida mai suna Nasiru Mohammed yace ya ga 'yan bindiga su na tserewa. Wannan harin, yayui kama da hare-haren sari ka noke da 'yan Boko Haram suka kai a baya.

Wani malamin makarantar Islamiyya a Bauchi, wanda ya ki bayarda sunansa, yace a yanzu kam ba su san ko su wanene 'yan Boko Haram, su wanene ba 'yan Boko Haram a cikin masu kai hare-hare ba. Yace, “su wanene ake kaiwa harin ne kam? Su wanene ke fakewa a bayan Boko Haram ne? Mun lura da cewa akwai dai wani abinda ke faruwa game da wannan lamari na Boko Haram” in ji malamin.

Wani mai fashin baki kan Afirka a wani kamfanin harkokin tsaro mai suna Control Risks, Thomas Hansen, yace a yanzu 'yan bindigar su na kai hare-hare a kan kauyuka ne su na kokarin su hana jama'a kakkafawa ko tallafawa kungiyoyin banga na fararen hula dake samun goyon bayan gwamnati a wannan yanki.

Sai dai kuma wasu masu fashin bakin sun yi gargadin cewa gwamnatin Najeriya tana kara ingiza jama'a su na goyon bayan 'yan Boko haram ta hanyar kashe wadanda ake zargi maimakon kama su, ko kuma kulle su na tsawon lokaci a cikin mummunan yanayin da har su na mutuwa ba tare da yi musu shari'a ba.

Tsohon jakadan Amurka a Najeriya, John Campbell, yace, “matakan nuna rashin imanin da gwamnati take dauka su na sanya jama'a tausayawa Boko Haram, abinda ke zama maida hannun agogo baya a wannan yunkurin.”
XS
SM
MD
LG