Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bafaranshen Da Ansaru Ke Garkuwa Da Shi A Najeriya Ya Tsere


Matar Francis Collomp, Anne-Marie Collomp, tana kallon labarin kubucewarsa a telebijin daga inda ta ke a tsibirin La Reunion.

Francis Collomp ya tsere daga inda ake garkuwa da shi a Zariya, ya hau Achaba zuwa ofishin 'yan sanda, bayan da ya shafe wata 11 a hannun 'yan kungiyar Ansaru

Bafaranshen da aka sace a yankin arewacin Najeriya watanni 11 da suka shige, ya kubuce daga hannun wadanda suke yin garkuwa da shi, ya hau Achaba zuwa ofishin 'yan sanda ba tare da an biya kudin fansa ko sisin kwabo ba.

Kwamishinan 'yan sanda na Jihar Kaduna, Olufemi Adenaike, yace Collomp ya kubuce daga hannun wadanda suke tsare da shi a birnin Zariya, inda aka maida shi kamar watanni uku da suka shige, ya kuma garzaya zuwa ofishin 'yan sanda a kan Achaba.

An sace Collomp ranar 19 ga watan disambar 2012, a lokacin da wasu 'yan bindiga su kimanin 30 suka abka cikin gidan da yake a garin Rimi a Jihar Katsina, kusa da bakin iyaka da Jamhuriyar Nijar. A lokacin, 'yan bindigar sun kashe wani makwabcinsa da wani maigadi. Kungiyar Ansaru, wadda ta balle daga jikin kungiyar Boko Haram ta dauki alhakin sace shi, har ma ta fitar da hoton bidiyonsa yana rokon da a taimaka domin a sako shi.

Shugaba Francois Hollande na Faransa, ya bayyana farin cikin ganin cewa Collomp ya kubutar da kansa, amma yace bai mance da wasu Faransawan su 7 ba wadanda ake yin garkuwa da su a Najeriya, Mali da kuma Syria.

Shugaban yace ministan harkokin wajen Faransa, Laurent Fabius, wanda yake tare da shi yanzu haka a wata ziyara a kasar Isra'ila, zai kama hanyar Najeriya nan take domin karbar Collomp.

Kwamishinan 'yan sanda na Kaduna Adenaike, yace jiya asabar Collomp ya tsere daga hannun wadanda ke yin garkuwa da shi din, kuma yau lahadi da safe suka mika shi hannun ofishin jakadancin kasar Faransa a Najeriya.

Kubucewar Collomp tana zuwa 'yan makonni kadan a bayan da aka sako wasu Faransawa 4 da kungiyar al-Qa'ida ta arewacin afirka ta yi garkuwa da su na tsawon shekaru uku a Jamhuriyar Nijar.
XS
SM
MD
LG