Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hare-haren Kunar Bakin Wake Sun Hallaka Mutane da Dama A Iraqi


Harin kunar bakin waken da aka kai akan wani wurin aikin gine gine da Iran ke kula dashi a garin Dibis a arewacin Iraqi yau juma’a, ya kashe mutane akalla 11.

Har wayau Yansandan Iraqi guda 6 da kuma mayakan Daesh ko ISIS 12 suka mutu a wani hari makamancin na Dibis a Ofishin Yansanda dake birnin Kirkuk.

A yayin da aka kai wa yansandan harin an ji karar fashewar nakiyoyi da kuma karar harbe harben bindigogi na fitowa daga harabar Ofishin yansandan. Faifan bidiyo da aka nuna a gidan talabijin da ke garin ya nuna bakin hayaki na tasowa daga harabar sannan da karar manyan bindigogi a ciki.

Kusan yan kunar bakin wake biyar ne suka kai hari a helkwatar yansandan, daya daga cikin su an harbe shi kafin bam din dake cikin rigar da ya saka ta tashi.

Daesh tace ita kai hari na farko. Amma har yanzu babu wanda ya dauki alhakin harin na biyu.

XS
SM
MD
LG