Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hare-haren Sojojin Amurka a Afirka Sun Kashe Shugabannin Mayakan Sa Kai Biyu


Sakataren Tsaron Amurka Ashton Carter
Sakataren Tsaron Amurka Ashton Carter

Rundunar sojin Amurka jiya Litinin ta ce farmakin data kai a baya bayan nan sun halaka shugabannin mayakan sakai su biyu a Afirka.

Kakakin ma'aikatar tsaron Amurka Pentagon Keftin Jeff Davis, yace harin da Amurka ta kai ranar 2 ga watan nan a Somalia ta sami nasarar kashe Abdirahman Sandhere, wani babba a rukunin shugabannin al-Shabab, shi da wasu mukarrabansa su biyu.

Davis yace mutuwar Sandhere, wanda kuma aka sani da inkiyar "Ukash," ya haddasawa al-Shabab babbar hasara da babban gibi.

Haka nan ma'aikatar tsaron ta Pentagon ta tabbatar da cewa wani hari da aka kai cikin watan jiya ya kashe Abukl Nabil, shugaban kungiyar ISIS a Libya.

Kakakin ma'aikatar yace, jirgin yaki samfurin F-15 ne ya kaddamar da harin kan Abul Nabil ranar 13 ga watan jiya a birnin Derna.Sai dai baiyi bayani kan irin jirgin yakin da aka yi amfani da shi wajen kai harin da Amurka ta kai a Somalia ba.

Ahalinda ake ciki kuma, wani jami'in gwamnatin Somalia yace hukumomin kasar sun kama wani dan kasar Amurka wanda dan kunigyar al-Shabab ne.

Hussein Mohammed Barre ya gayawa Sashen harshen Somalia na Muryar Amurka cewa mutumin yayi saranda ne ga jami'ai da kuma sojojin kiyaye zaman lafiya na kungiyar hada kan kasashen Afirka a garin Baraware dake kan gabar ruwa.

XS
SM
MD
LG