Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hari Kan Gwamna Ortom: Gwamnonin Jihohin Arewa Sun Dauki Mataki


Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom.
Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom.

Kungiyar gwamnonin Arewacin Najeriya tace za ta baiwa sabbin shugabannan tsaro goyon baya don kawo karshen ayyukan ta’addanci a Najeriya

Shugaban kungiyar kuma gwamnan jahar Pilato, Simon Lalong yace shugaban kasa Muhammadu Buhari​ ya bada umurnin samo jiragen da zasu taimaka wajen dakile matsalar tsaro a kasar.

Matakin na zuwa ne a dai dai lokacin da gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, yace wasu ‘yan bindiga sun kai masa hari a ranar Asabar, amma ya tsallake rijiya da baya.

ba-za-mu-amince-da-kai-hari-akan-dayanmu-ba---gwamnonin-najeriya

yan-bindiga-sun-kai-wa-gwamnan-benue-samuel-ortom-hari

Kwamishinar yada labarai da yawon shakatawa a jahar Binuwai, Madam Ngunan Adingi tace tuni gwamnan jihar ya rubuta takardar koke ga shugaban kasa.

Taron Gwamnoni Arewacin Najeriya A Jihar Kaduna
Taron Gwamnoni Arewacin Najeriya A Jihar Kaduna

A bangare guda kuwa kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore, da gwamna Ortom ya bukaci a kame shugabannan ta bisa zargin kokarin hallaka shi, ta maida martani ta bakin shugabanta, Alhaji Bello Bodejo wanda yace basu da wata masaniya kan harin.

Karin bayani akan: Shugaba Muhammadu Buhari​, jihar Benue, Samuel Ortom, Nigeria, da Najeriya.

A hirar shi da Muryar Amurka, Bello Bodejo ya ce Kungiyar Miyellti Allah Kautal Hore, ba kungiyar ta'addanci ba ce. Bisa ga cewarshi, gwamna Ortom ya zargi kungiyar da ta'addanci tun lokacin da ya kafa doka, su ka kuma nemi tattaunawa da shi sabili da bisa ga cewarshi, ba bu adalci a dokar sabili da babu wurin da aka ce Fulani ba za su iya cin moriya ba. Bodejo ya ce wannan zargi ne sabili da haka babu hannun kungiyar su a cikin lamarin.

Saurari rahoton Zainab Babaji cikin sauti:

Hari Kan Gwamna Ortem: Gwamnonin Jihohin Arewa Sun Dauki Mataki-3:00"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:01 0:00


  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG