Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hari: Shugaban Benizuwaila (Venezuela) Ya Auna Arziki


Shugaban Benizuwaila (Venezuela) Nicolas Maduro a wurin jawabin

Dambarwar siyasar kasar Benizuwaila dai ta dau wani sabon salo mai ban tsaro bayan da aka auna Shugaban kasar da wasu 'yan mitsi-mitsin jiragen sama da ke dauke da bama-bamai

Shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro ya tsallake rijiya da baya, a wata tarwatsewar da wasu ‘yan mitsi-mitsin jiragen sama biyu marasa matuka su ka yi daura da inda ya ke karanta jawabinsa ga kasar ta gidan talabijin a birnin Caracas jiya Asabar.

Hotunan talabijin sun nuna yadda Shugaba Maduro da sauran jama’ar da ke wurin su ka kadu yayin da ake ta jin karar fashe-fashe. ‘Yan dakikoki kadan sai aka ga su kansu sojoji na ta-kai ta-kai.

Rahotanni na nuna cewa sojoji akalla 7 ne su ka ji raunuka.

Daga bisani Ministan Yada Labaran kasar ya yi jawabi ta gidan talabijin na kasar inda ya jaddada cewa Shugaba Maduro na nan lafiya lau, kuma ya na kan halartar wani taron jami’an gwamnatinsa, a yayin da ake kan jinyar wadanda su ka ji raunuka.

Kasar Venezuela dai na fama da mummunar dambarwar siyasa da ta tattalin arziki.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG