Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

SYRIA: An Kashe Shugaban Rundunar Mayakan Tawaye Ta Jaish


Marigayi Shugaban Mayakan Sa Kan 'Yan Tawayen Syria ta Jaish Army, Zahran Alloush
Marigayi Shugaban Mayakan Sa Kan 'Yan Tawayen Syria ta Jaish Army, Zahran Alloush

An hallaka daya daga cikin jiga-jigan shugabannin kungiyoyin ‘yan tawayen Syria a wani harin da aka kai ta sama a kusa da Damuscus babban birnin kasar. Dakarun kasar sun ce sune da alhakin kai harin saman a jiya Juma’a.

Wanda kuma harin ya kashe Zahran Alloush wanda ya assasa sojojin yakin sa kan da aka fi sani da Army of Islam, sannan harin ya hallaka har da ma wasu da dama daga shugabannin kungiyar.

Wata kingiyar sa ido a rikicin Syria da rajin kare ‘yancin Bil’adama mai matsuguni a birtaniya tace, harin saman ya dira a shelkwatar mayakan na Army of Islam ne a garin Otaya da ke kusa babban birnin na Syria.

Ya kuma kashe da dama daga shugabannin kungiyar ciki har da shi Alloush a lokacin da suka taru don yin taron kungiyar tasu. Tuni dai har kungiyar ta maye gurbin Alloush da wani Dakarensu Essam el-Buwaidani da aka fi sani da Abu Hammam.

Hira Da Dakta Faruk Bibi Faruk Akan Matsalar Tsadar Rayuwa A Najeriya Kashi Na Biyu
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG