Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Harin al-Shabab Ya Hallaka Mutane 12 Kan Iyakar Somalia da Kenya


Wurin da aka kai hari a garin Mandera

Wani harin da masu tsattsauran ra’ayi suka auna kan wasu da ba musulmi ba, a arewa maso gabashin iyakar Kenya da Somaliya yau Talata, ya halaka mutane 12, a cewar wani jami’in kasar.

‘Yan bindigar al-shabab da mazauninta ke Somali sun kai hari kan masaukin baki dake wurin da ake kira Bisharo, a karamar hukumar Mandera. Sun yi amfani da gurneti da kuma wasu ababen fashewa, a cewar kwamandan yankin Job Boronjo.

Boronjo yace “lallai an kai hari, kuma ma’aikatan agaji na kan aiki yanzu haka.

Ba tare da bata lokaci ba kungiyar al-Shabab ta dauki alhakin kai harin a kafar yada labaranta. Ta ce ta kai harin ne a kan kristocin da suke aiki a wurin.

Harin da aka kai yau Talata shine na baya-bayan nan a jerin hare haren da al-Shabab ta kai tsallaken iyaka, tun bayan da kasar Kenya ta kutsa cikin rikicin da ake yi a Somaliyya a shekarar 2011.

A farkon watan nan an kashe mutane 6 a wani hari makamancin wannan da aka kai a kan wasu baki a garin na Mandera lokacin da wasu da ake zaton ‘yan al-Shabab ne suka kai hari a unguwar.

A watan Nuwambar shekarar 2014, mayakan suka kashe mutane 28 wadanda ba musulmi ba ne, bayan da suka kame wata bus a garin na Mandera.

Haka nan a Somaliyan ma, wani dan harin kunar bakin wake da ake zargi dan al-Shabab ne, ya tada nakiyoyi da aka dankarawa wata motar dakon kaya a sansanin sojojin kiyaye zaman lafiya na kungiyar hada kan Afirka, ya kashe akalla mutane uku. Wasu mutane biyar kuma sun jikkata.

Sakataren Gwamnatin kasar Amurka Michael R. Pompeo

Magoya Bayan Trump Sun Afkawa Ginin Majalisun Amurka

Magoya Bayan Shugaba Donald Trump Sun Mamaye Ginin Majalisar Dokokin Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:56 0:00

Rayuwar Birni

Rayuwar Birni: Hira da Aliyu Danlami mai sayar da furanni a Abuja
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:49 0:00
Karin bayani akan Rayuwar Birni
XS
SM
MD
LG