Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Harin Bam A Biu Ya Hallaka Mutane Wajen 8


Taswirar Nijeriya mai nuna inda garin Biu ya ke a jihar Borno

Mutane wajen 5 zuwa 8 ne ake kyautata zaton sun mutu a wasu tagwayen hare-haren bama-baman da aka kai yau Talata a garin Biu na jihar Borno, baya ga wasu da dama da su ka ji raunuka.

Wasu tagwayen bama-bamai sun tashi a mashigar garin Biu, mai tazarar kilomita 187 daga Maiduguri babban birnin jihar Borno, a yau dinnan da misalin karfe 1, da su ka yi sanadin mutuwar wasu mutane da raunata wasu.

Wakilinmu a Maiduguri Haruna Dauda Biu, wanda ya aiko da rahoton, ya ce wannan ne karo na biyu cikin mako guda da aka kai harin na bam a garin na Biu, inda a makon jiya wata ‘yar kunar bakin wake ta tarwatsa kanta a cikin wata kasuwa ta hallaka mutane 8.

Haruna ya ce shaidun gani da ido sun gaya masa cewa sun ga gawarwakin mutane da dama a kwance a harin na yau, inda wasu ke cewa mutane wajen 8 ne su ka mutu, wasu kuma ke cewa kimanin mutane 5 ne su ka mutu. Y ace ya yi kokarin jin ta bakin hukumomin tsaro amma bai yi nasara ba. To amma ya ruwaito shaidun gani da ido na bayyana abin da su ka gani na gawarwaki da kuma barnace-barnace iri-iri.

please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:04:41 0:00
Shiga Kai Tsaye

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG